26 Mayu 2020 - 07:14
Jirgin Dakon Mai Na 2 Da Iran Ta Aika Ya Isa Gabar Ruwan Kasar Venezuela

Rahotanni sun bayyana cewa Jirgin ruwan dakon mai na kasar Iran na biyu mai suna Farsar ya isa yankin ruwan kasar Venezuela tare da rakiyar jiragen ruwan kasar,

(ABNA24.com) Rahotanni sun bayyana cewa Jirgin ruwan dakon mai na kasar Iran na biyu mai suna Farsar ya isa yankin ruwan kasar Venezuela tare da rakiyar jiragen ruwan kasar, tuni dai jirin ruwan dakon main a Iran na farko mai suna Furuchun da shi ma ya samu rakiyar jiragen ruwan sojin kasar ta Venuzuela ya fara isa gabar ruwan ,kuma ana saran a nan gaba kadan jirgin sai sauke manda yake dauke da shi a tashar jirgin ruwan kasa ta Venezuela

Yanzu haka ma jirgin ruwan dakon mai din na 3 na kasar Iran me suna Faksun yana kan hanya da ake sa rana nan da 27 ga watan da muke cikin zai isa gabar ruwan kasar ta Venezuela inda shi ma zai samu rakiyar jiragen ruwa dakarun sojin kasar ,

A makon da ya gabata ne wani jami’in Gwamnatin Amurka ya sanar cewa za su dauke mataki kan jiragen ruwan dakon mai Iran za ta aike da shi zuwa kasar Venezuela.

Bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Venezuela ta fitar jim kadan bayan Isar Jirgin dakon mai na farko da Iran ta aike, ya nuna cewa kasshen biyu za su ci gaba da yin aiki tare wajen karya takunkumin kasar Amurka


/129